[0:00]Ga tsananin ga tsananin ku. Akwai wani yaro mai suna Mahmud. Mahmud yaro ne mai kokarin gaske, baya wasa da karatun sa. Wata rana bayan an tashi daga makaranta sai abokin sa wato Zaid, yace dan Allah ka aramin littafin ka. Sai abokin sa Zaid yace masa dan Allah ka aramin littafin ka. Zankafo rubutun da akayi bana nan. Sai Mahmud yace to gashi amma akwai aikin gida da malama ta bamu a ciki. Kar ka kopa amsoshe na kaji. Zaid yace babu matsala bazan ma bude shafin ba. Washe gari a aji da malama ta shigo. Sai ta kira sunan Mahmud da Zaid, tace wadannan yaran sun kafa junan su saboda haka sai na hukunta su. Sai Mahmud yace wa malama gaskiya malama na ara wa Zaid littafi na. Amma sai da yayi mun alkawari cewa bazai kofa amsoshi na ba shiyasa na bashi. Malama tace Zaid hakane? Zaid yace hakane malama. Malama tace Mahmud je kazauna amma ka kiyaye a gaba. Kai kuma Zaid kaje ka share farfajiyar makarantar tsaf, hukuncin ka kenan. Da aka tafi hutun cin abinci Zaid ya kuma zuwa ya samu Mahmud. Yace dan Allah Mahmud kayi hakuri bazan sake kofar amsoshinka ba. Zaka iya aramin littafin ka kar ka damu. Bazan kofe ka ba. Sai Mahmud yace to, in mun tashi daga makaranta kazo in baka. Sai Mahmud ya rubuta amsoshin da ba daidai bane da gangan saboda yasan Zaid zai sake kofarsa. Sai ko washe gari malama ta sake kirawo sunayensu. Tace kowa yaci goma goma a ajin nan amma banda Mahmud da Zaid. Naga kuma sun kofa junan su basu ci ko daya ba. Saboda haka yau zasu share dukkanin azuzuwun makarantar nan kafin su tafi gida. Bayan sun gama aikin da aka sasu, sai Mahmud yaje ya samu yayar sa Hasina yana ta kuka. Hasina tace me ya same ka? Yace yaya Hasina, garin nako yawa Zaid hankali. Na faɗi a aikin da malama ta bamu ban ci ko ɗaya ba gashi ta hukuntamu. Na rubuta amsoshin da ba daidai ba. Sai Hasina tace, daman ance idan zaka gina ramin mugunta, to ka gina shi ga jere. Bari in baka wani labari. Akwai wani kwado da bera da suke abota. Kullum sai kwado ya kai wa bera ziyara. Sai bera ya dafa abinci kala kala masu dadi, su ci su sha. Da daddare sai kwado ya tafi gida. Wata rana sai kwado yace, wai ni kullum sai dai in je gidan bera. Shi bazai zo inda nake ba? Ai wannan rainin hankali ne. To zan ko koya masa hankali. Sai kwado yaje gidan bera, yace abokina yau a gida na zamuyi wasa. Sai bera yace karfa ka manta gidan ka a cikin ruwa yake kwado. Ni kuma bazan iya rayuwa a ruwa ba. Kuma gidan ka akwai nisa, ni ina saurin gajiya. Sai kwado yace haba kar ka damu. Ai ba sai kayi wahala ba. Zan ɗaure kafa ta da kafar ka sai in ja ka mu tafi. Kuma bazan shigar da kai cikin ruwa ba. Sai mu ɗan yi wasan mu a gefen ruwan. Bera ya ɗanyi jim. Can yace to abokina mutafi. Kwado ya samo igiya ya ɗaura a kafarsa, ya ɗaura ɗaya bangaren na igiya a kafar bera. Ya ja bera suka tafi. Da suka isa gurin ruwan sai bera yace to mu tsaya a nan kar ka kaini cikin ruwa, ni ban iya ruwa ba. Kwado yayi kunnin uwar shegu, ya ja bera suka shiga ruwa. Bera ya dinga tambal tambal yana cewa dan Allah ka maida ni waje kar na mutu. Kwado ya ki ji. Har sai da bera ya sha ruwa ya mutu. Sai jikin bera yayyo saman ruwan. Amma kwado ya manta bai kwance wanan igiyar da ya ɗaura masa ba. Yayi ta dariya yana cewa ai nayi maganinka. Can sai ga wata mikiya ta hango gawar bera yana yawa a saman ruwa. Sai tace la ga nama. Sai ko ta sauka ta ɗauko bera. To da yake a ɗaure suke da kwado. Kwado sai ji yayi ana ja sa. Mikiya taga ta ɗauko bera ga kuma kwado. Tayita murna, ta kai su saman bishiya ta cinye gawar bera sannan ta cinye kwado. Mahmud yace gaskiya ne Hasina. Idan zaka gina ramin mugunta, to ka gina shi ga jere domin kai ma zaka iya fadawa. Da na sani kawai na hana shi littafi na. Ban rubuta amsoshin da ba daidai ba. Gashi nan nima na samu hukunci. Amma daga yau na koyi darasi nagode Hasina. Kurungus, kan ɗan bera.

Tatsuniyar Bera da Kwado / Hausa Stories for Kids / Bedtime stories for kids
Voice of Anani
4m 58s756 words~4 min read
Auto-Generated
Watch on YouTube
Share
MORE TRANSCRIPTS


